Sau nawa Obasanjo na yi wa shugabannin kasa baki? - Knock Media™

Breaking

Ads

BANNER 728X90

Saturday, 27 January 2018

Sau nawa Obasanjo na yi wa shugabannin kasa baki?

Masana harkokin siyasa sun ce wasikar da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari tamkar wata al'ada ce ta tsohon shugaban.

A farkon makon nan ne Cif Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari budaddiyar wasika inda ya soke shi bisa abin da ya kira rashin iya shugabancinsa.

Mr Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ba zai iya fitar wa Najeriya kitse a wuta ba don haka bai cancanci yin wa'adi biyu na shugabancin kasar ba.

Daga nan ne tsohon shugaban ya yi kira a gare shi da ya ajiye mulki idan wa'adinsa na farko ya kare sannan ya bi sahun tsoffin shugabannin kasar wajen bayar da shawarwari kan yadda za a gyara Najeriya.

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa Bashir Baba ya shaida wa BBC cewa tsohon shugaban kasar "tamkar tauraruwa mai wutsiya ce, wacce Hausawa kan ce ganinki ba alheri ba."

Shin Obasanjo yana shirin kafa wata kungiyar siyasa ce?

Obasanjo ya kushe gwamnatin Buhari
"Wannan ba shi ne karon farko da wannan dattijo ke sukar shugabannin da ke mulki ba. Ya soji Alhaji Shehu Shagari da Janar Ibrahim Babangida da Janar Sani Abacha. Sukar da ya yi wa Abacha ce ta sa aka daure shi.

"Bayan ya sauka daga shugabancin kasa a shekarar 2017, Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua, wanda shi ya dora shi a mulki, ya hau sai da Cif Obasanjo ya soke shi.

Haka kuma ya soki Dr Goodluck Jonathan," in ji Bashir Baba.

Ya kara da cewa kusan duk lokacin da Cif Obasanjo ya soki shugaba mai-ci shi ne da gaskiya, amma duk da haka "shi kansa bai iya yin mulki irin wanda yake son wasu su yi ba. Da alama yana ganin shi ne ya fi kowa iya mulki."

No comments:

Post a Comment