MANOMAN SHINKAFA DA AMBALIYAR RUWA TA SHAFA BARA ZASU DARA-CBN. - Knock Media™

Breaking

Ads

BANNER 728X90

Wednesday, 16 January 2019

MANOMAN SHINKAFA DA AMBALIYAR RUWA TA SHAFA BARA ZASU DARA-CBN.


Kungiyar manoman shinkafa ta kasa RIFAN ta ce babban bankin kasar nan CBN ya amince da biyan tallafi ga manoman shinkafa dubu 550  da suka tafka asara sanadiyyar ambaliyar ruwa a bara.

Shugaban kungiyar ta RIFAN Aminu Goronyo ne ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ya ce gwamnan na CBN ya bada umarnin a sake fasalin bashin da aka bawa manoman zuwa shekaru  hudu.

Aminu Goronyo ya ce manoman shinkafar dake karkashin shirin RIFAN da CBN ne kawai zasu amfana da wannan tallafi.

Ya ce an dauki wannan mataki ne biyo bayan kamala taron musamman da daraktan sashin kudade na bankin da kuma jami’an RIFAN.

Y ace kungiyar su ta RIFAN ta bibiyi hakkin wadanda ke karkashin ta ne kawai ta tsarin nan na Anchor Borrowers kuma sune wadanda za a biya wannan tallafi.

Aminu Goronyo ya ce a binciken da suka yi a jihohin da ambaliyar ruwan ta shafa, sun tantance  masifar ta  shafi dubunnan hectar gonakin shinkafa da masara.

No comments:

Post a Comment