Wani sabon binciken kimiyya ya nuna cewa za a iya amfani da ganyayyaki da itacen Agwaluma wajen magance zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani.
Binciken wanda aka wallafa a kundin
BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.
Masu binciken wadanda ‘yan Nijeriya ne sun gwada ingancin maganin a akan beraye da ke dauke da cutar, idan aka samu nasarar magance ta daga jikin su.
Masanan sun ce a nan gaba akwai yiwuwar za a koma amfani da saiwar Agwaluma da ganyayyakin ta wajen hada magungunan Malaria.
No comments:
Post a Comment