ZABEN GWAMNAN KANO: KOTU TA YI WATSI DA KARAR DAKE KALUBALANTAR TAKARAR ABBA KABIR YUSUF - Knock Media™

Breaking

Ads

BANNER 728X90

Wednesday, 16 January 2019

ZABEN GWAMNAN KANO: KOTU TA YI WATSI DA KARAR DAKE KALUBALANTAR TAKARAR ABBA KABIR YUSUF

Wata Babbar kotun Kano ta kori karar da aka shigar gaban ta ana kalubalantar Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Kotun wadda ke zama a sakatariyar Audu Bako karkashin mai shari’a A T Badamasi ta yanke hukuncin korar karar da aka shigar kan dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP Engr. Abba Kabir Yusuf, a zaman kotun na yau.

Kotun ta tabbatar da injiniya Abba Kabiru Yusuf a matsayin cikakken dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan dake tafe na 2019.

Da yake zaman yanke hukuncin yau, mai shari’a A T Badamasi ya yi watsi da karar da Jaafar Sani Bello ya shigar yana kalubalantar Injiniya Abba Kabir bayan zaben fitar da gwani ranar 1 ga oktoban bara a nan Kano.

Jafar Sani Bello ya nemi kotun ta ayyana shi a matsayin halastaccen dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a Kano a zaben 2019 dake tafe.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadaan bayan yanke hukuncin, lauyan wanda akai kara Barista  Bashir Yusuf Muhammad ya ce basu yi mamakin hukuncin ba duba da  irin hujjojin da suka gabatarwa kotun.

A nasa bangaren lauyan masu kara barista Abdul Adamu Fagge ya ce zasu tattauna kan hukuncin da wanda yake karewa domin daukar mataki na gaba.

No comments:

Post a Comment