Maigirma shugaban 'Yan Sandan Kasarmu Nijeriya IGP Ibrahim K. Idris shine na 19 a tarihin manyan sufetan 'Yan sandan kasar Nigeria da suka shugabanci rundunar.
IGP Ibrahim K Idris kullum burinsa yayi abin alheri a hukumar 'Yan sanda wanda ko bayan wa'adinsa ya kare za'a dinga tunawa da shi, muna kara yi masa fatan alkairi a ko yaushe.
Yana da gaskiya da amana ga jajircewa, hakan ne yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari yake aiki da shi domin yasan waye Ibrahim K Idris a tarihin aikinsa na 'Yan sanda, bashi da wasa ko kadan musamman wajen yaki da cin hanci, kuma baya daga kafa ga masu aikata miyagun laifuka.
Manya da Kananun yansanda suna jin dadin aikinsa domin yana kyautata musu yadda ya kamata, IGP Ibrahim K Idris bai san hanawa ba kullum bayarwa ya sani, yana bakin kokarinsa wajen yin abinda yake shine na gaskiya.
Manyan 'yan siyasa irinsu Bukola Saraki sun saka IGP Ibrahim K. Idris a gaba saboda abinda suka aikata na manyan laifuka, har daukar nauyin kungiyoyi sukayi domin ayi zanga zangar da za ta sa shugaba Buhari ya sallami IGP Ibrahim K. Idris, ba da jimawa ba Dino Malaye yace IGP yana so zai masa allurar mutuwa, Bukola Saraki ya fito yace shima IGP Ibrahim yana bibiyar rayuwarshi.
Haka dai suma saka wannan hazikin 'dan sanda a gaba, suna masa sharri da batanci domin ganin an saukeshi daga mukaminsa, su a yadda sukaso basu so ya kawo war haka a matsayin IGP ba, kuma da dukkan alama burinsu ya cika kamar yadda labari yake fitowa Buhari ya nada sabon IGP.
Muna Addu'ah Allah Ya sa IGP Ibrahim K. Idris ya wanye da aikin lafiya, Allah Ya sa ya zama sila ta shigar sa Aljanna da duk masu halin kwarai irin nasa. Amin.
No comments:
Post a Comment