Wata babbar kotun tarayya a nan Kano, karkashin mai shari’a Sa’a Ibrahim ta soke zaben da aka yiwa Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin dan takarar majalisar wakilai na karamar hukumar birni karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Alkalin kotun ta kuma ce sashi na uku na dokar zabe ta kasa y ace jam’iyyar siyasa bata da ikon sauya sunan dan takara.
A jawabin sa lauyan mai kara wato Muktari Ishaq Yakasai, Barista Ibrahim Waru ya bayyana godiyar sag a kotun saboda tsayawa kan gaskiya domin ta ga adalci ya tabbata.
Shi kuwa a nasa bangaren lauyan wanda ake kara Barista Nuraini Jimoh ya ce zasu daukaka kara kan wannan hukunci.
No comments:
Post a Comment