Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta dakatar da gwamnatin tarayya daga ci gaba da shirin gurfanar da babban jojin Najeriya mai shari’a Walter Onnoghen a gaban kotun da’ar ma’aikata wato CCT.
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar da’ar ma’aikata ta shirya wasu tuhume-tuhume guda shida da suka danganci kin bayyana kadarorin da babban jojin na Najeriya ya mallaka.
A yau litinin ne aka shirya gurfanar da shi gaban kotun ta da’ar ma’aikata, amma bai halarci kotun ba.
Da yake yanke hukunci kan wasu bukatu biyu da aka gabatar masa a yau litinin, mai shari’a N E Maha na babbar kotun tarayyar, ya umarci bangarorin biyu da kowa ya tsaya a matsayin sa har zuwa 17 ga watan da muke ciki.
Ya kuma yanke hukuncin cewar dukkaan wadanda ake karar dole ne a mika musu takardar sammaci kuma su bayyana a zaman kotun na gaba.
Wadanda suka shigar da karar karkashin Center for justice and peace initiative sun sanya sunan ministan shari’a Abubakar Malami da shugaban kotun ta da’ar ma’aikata Danladi Umar da hukumar lura da harkokin alkalai da babban sufeton ‘yan sanda da kuma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki cikin wadanda ake kara.
Mai shari’a Maha ya ce kada wanda ya dauki wani mataki kan wannan batu har sai ranar 17 ga watan da muke ciki, kuma dukkan bangarorin biyu su je kotun domin sauraron wannan kara.
An dai bada wannan umarni ne jim kadan bayan da kotun da’ar ma’aikata ta fara zaman sauraron shari’ar ta babban jojin Najeriya Walter Onnoghen.
No comments:
Post a Comment