'Sauyin yanayi 'ya fi yi wa mata illa fiye da maza' - Knock Media™

Breaking

Ads

BANNER 728X90

Saturday, 10 March 2018

'Sauyin yanayi 'ya fi yi wa mata illa fiye da maza'

Wani sakamakon bincike da aka gudanar ya nuna sauyin yanayi ya fi yi wa mata illa fiye da maza.

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, kashi 80 cikin dari na mutanen da sauyin yanayi ya raba da gidajensu mata ne.

Saboda matsayin mata na iyaye da ke hidima da ayyukan gida ne ke sa suka fi shan wahala a duk lokacin da aka samu ambaliya da fari.

A Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda kusan kashi 90 cikin 100 na tafkin Chadi ya kafe, 'yan asalin yankin suna cikin hadari. mata sai sun yi tafiya mai nisa kafin su debo ruwa.

"A lokacin rani, maza na fita ne zuwa gari, sai su bar mata don su kula da gida," a cewar Hindou Oumarou Ibrahim, shugabar wata kungiyar Mata da al'ummar Chadi.

A yayin da yanzu ake samun lokacin rani mai tsawo, mata suna shan wahala wajen kula da gida ba tare wani taimako ba. " Matsalar ta fi shafar su... aiki ne mai wahala sosai," kamar yadda Hindou ta shaidawa shirin Mata 100 na BBC.

Matsala ce a duniya

Wannan ba matan karkara ba ne kawai matsalar ta shafa, Mata a duniya baki daya na iya fuskantar wannan kalubalen, kuma ba su da wani karfin fada aji fiye da maza. Wannan ya sa yana da wahala a iya farfadowa daga bala'oin da suka shafi gidaje da ayyuka da abubuwan more rayuwa.

Bayan guguwar Katrina a shekara 2005, Mata bakaken fata a Amurka suna cikin wadanda ambaliya ta fi yi wa illa Louisiana.

"ANew Orleans, Mata bakaken fata sun fi fama da talauci kafin guguwar Katrina," a cewatr Jacquelyn Litt, farfesar ilimin mata da jinsi a Jami'ar Rutgers.

Ta shaidawa BBC cewa "Matan da ba su da aure ke jagorantar kusan rabin yawan gidajen da talauci ya fi yin katutu."

Bala'o'in da aka fuskanta ana ganin su ne suke haifar da yawaitar matsalar cin zarafin mata da ake samu da suka hada da fyade.

No comments:

Post a Comment