Jirgin Arik ya yi saukar gaggawa a Ghana - Knock Media™

Breaking

Ads

BANNER 728X90

Saturday, 10 March 2018

Jirgin Arik ya yi saukar gaggawa a Ghana

Wani jirgin sama mallakar babban kamfanin sufurin jiragen sama na Arik a Najeriya, ya yi saukar gaggawa yayin da direban jirgin ya farga cewa hayaki yana fitowa daga bangaren da fasinjoji suke.

Jirgin ya tashi ne daga Legas ya nufi birnin Accra na kasar Ghana, amma sai hayakin ya rika fitowa a yayin da jirgin ke sama kafin ya kai ga ainihin inda zai sauka.

Hakan ya auku ne bayan da aka sami aukuwar irin wannan lamari har sau biyu, wadda ta shafi kamfani sufurin jiragen sama na Dana a Abuja da Fatakwal.
Daya daga cikin fasinjan jirgin da ya yi saukar gaggawar ne ya kwarmata labarin a kafar sada zumunta ta intanet.

Fasinjan ya yi korafi kan yadda aka zalunce shi da sauran fasinjojin da abin ya shafa, yayin da a karshe jirgin ya sauka a kasar Ghana, bayan wanzuwar lamarin.

Sai dai a wani bayani da kamfanin sufurin jiragen saman na Arik ya yi, ya ce ba a sami aukuwar wani hadari ba, kuma fasinjojin sun sauka daga jirgin ba tare da wata matsala ba.

Wani mai magana da yawun kamfanin na Arik, Adebanji Ola ya ce, direban jirgin saman ya yi wa fasinjojin da ke cikin jirgin bayanin abin da ya auku, kuma ya kwantar masu da hankali.

Sannan ya ce deireban ya yi amfani da ingantattun matakan da suka kamata wajen sarrafa jirgin, yayin da hayaki ya rika fitowa daga wata kafa da ba a sani ba a bangaren da fasinjoji suke, a lokacin da ya rage saura mil tamanin da daya jirgin isa birnin Accra, a ranar Talatar da ta gabata.

Matalar dai ta tilastawa kamfanin Arik ajiye jirgin da hayaki ya rika fitowa a cikinsa a can kasar Ghana, kuma kamfanin ya ce ya tura tawagar injiniyoyi don su duba shi, su tantance musabbabin matsalar.

Hakan dai ya faru ne, bayan aukuwar jerin wasu lamura da saura kadan su zama abin kaico a harkar sufurin jiragen sama ta Najeriya a 'yan makwannin da suka gabata.

A makwannin da suka gabata ne daya daga cikin kamfani sufurin jiragen sama na Dana ya abka daji bayan ya sauka a garin Fatakwal.

Wannan dai yanyo ana kiraye-kiraye ga gwamnatin Najeriya kan ta mayar da hankali sosai ga bangaren harkar sufurin jiragen sama na kasar.

Sai dai kuma nata gangaren gwamnatin ta ce ta bayar da umarnin a binciki yadda kamfanin sufurin jiragen sama na Dana yake gudanar da ayyukansa.
Source  bbc

No comments:

Post a Comment